Tsakanin 'yan ci rani 7,000 da 8,000 daga yankin kudu da hamadar Sahara ne ake tsare da su a wasu cibiyoyi tsugunar da 'yan gudun hijira a Libya.
Jami'in hukumar yaki da bakin haure ta Libya Abdulrazaq Al-shniti ne ya bayyana haka a jawabinsa yayin bude sabuwar cibiyar tsugunar da 'yan hijira a Tajura dake yammacin Tripoli.
Al-shniti ya ce, yadda iyakar kudancin Libya ke a bude, shi ne dalilin da ya sa ake samun kwararar bakin haure.
Ya kara da cewa, ana mai da bakin kasashensu, bayan shirya da ofisoshin jakadancin kasashensu da kuma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta duniya dake ba da taimako ga cibiyoyin tsare bakin.
Ya kara da cewa, za a iya takaita kwararar bakin hauren ne idan aka hana su tsallaka iyakar dake kudancin kasar.
Libya ta kasance hanya ga 'yan ci rani dake son tsallakawa kogin Mediterranean zuwa Turai.
Masu fasa kauri na amfani da halin rikici da rashin tsaro da ake fama da shi, wajen safarar dubban 'yan ci rani zuwa Turai, inda galibinsu ke nutsewa a kan hanya. (Fa'iza Mustapha)