in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan zurfafa hadin gwiwa a fannin bunkasa rayuwar mata
2017-04-27 09:41:54 cri

Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong, ta ce kasar ta na fatan zurfafa hadin gwiwa da kasar Afirka ta kudu, a fannin inganta rayuwar mata.

Madam Liu wadda ke ziyarar aiki a Afirka ta kudun, ta bayyana hakan ne yayin da ta halarci bikin mika kyaurar wasu kekunan dinki, da hadaddiyar kungiyar matan kasar Sin ta ACWF ta gabatar, ga kungiyar matan jam'iyyar ANC mai mulki a Afirka ta kudun.

Ta ce Sin da Afirka ta kudu kasashe ne masu tasowa, wadanda kuma ke samun ci gaban tattalin arzikin su sannu a hankali. Don haka a cewar ta hadin gwiwar sassan biyu baya ga fadada ci gaba mata, zai kuma samar da zarafi na cimma nasarar kudurorin daidaiton jinsi.

Daga nan sai ta bayyana shirin kasar Sin, na ci gaba da musaya tare da Afirka ta kudu, game da burin cimma nasarar samarwa mata ilimin bai daya, da batun inganta kiwon lafiya, da yaki da talauci, tare da kara samar da damammaki na daidai-wa-daida tsakanin al'ummomin duniya.

Madam Liu ta kara da cewa Sin na fatan karin kungiyoyin mata za su shiga a dama da su, cikin manufofin hadin gwiwar Sin da Afirka ta kudu, musamman a fanni musaya tsakanin sassan biyu, su kuma tallafa wajen tabbatar da nasarar ci gaban rayuwar mata a dukkanin fadin duniya.(Saminu Alhasan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China