A jiya Laraba bankin duniya ya bukaci kasashen dake kudu da hamadar Sahara ta nahiyar Afrika da su aiwatar da tsare tsare masu kyau wadanda za su tabbatar da zuba jari a fannin kayayyakin more rayuwa domin tattalin azrikin shiyyoyin ya samu bunkasuwa.
A cewar sabuwar kididdigar game da Afrika wadda bankin duniyar ya gudanar, idan aka inganta wasu tsare tsare marasa inganci, sannan aka samu hadin gwiwar gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu wajen samar da ababan more rayuwa, hakan zai kasance tamkar wata muhimmiyar dabara ce ta yakar talauci da kuma samun bunkasuwar tattalin arziki.
Punam Chuhan-Pole, babban jami'i masanin tattalin arziki mai kula da shiyyar Afrika a bankin duniya kuma mawallafin wannan rahoto, ya bayyana cewa, hadin gwiwar gwamnatoci da hukumomi masu zaman kansu a kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika ya kasance tamkar wata karamar kasuwa ce, wadda ta mayar da hankali kan samar da tsare tsare a kasashe yan kadan da suka hada da Afrika ta Kudu, Najeriya, Kenya da Uganda.
Chuhan-Pole ya fada a lokacin kaddamar da rahoton a Nairobi cewa, kididdiga ta nuna cewa, tasirin zuba jari na gwamnatoci yana samar da bunkasuwar tattalin arziki ne idan kasashen suka aiwatar da tsare tsaren da za su ba da damar samun ingantuwar shirye shiryen yadda ya kamata.
Bankin duniyar ya bayyana cewa, kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika suna fuskantar tafiyar hawainiya ta fuskar zuba jari da kusan kashi 8 cikin 100 a shekarar 2014 zuwa 0.6 ciikin 100 a 2015, ya kara da cewa, wannan jan kafar da ake samu ta fuskar zuba jarin ya ci karo da manufar tsara ci gaban tattalin arzikin Afrika.
Ya ce, batun samar da kayayyakin more rayuwa ya kasance muhimmin batu, duba da yadda nahiyar ke da dunbun bukatunsu domin gudanarwar al'amurra yadda ya kamata.(Ahmad Fagam)