in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya yi hasashen bunkasuwar tattalin arzikin yankin kudu da Sahara da kashi 2.6 a 2017
2017-04-20 09:52:43 cri

Bankin duniya ya yi hasashen samun bunkasuwar tattalin arzikin kasashen kudu da hamadar Saharar Afrika da kashi 2.6 cikin 100 a shekara 2017, kashi 3.2 ciki 100 a shekarar 2018, da kuma kashi 3.5 cikin 100 a shekarar 2019.

Bankin ya bayyana hakan ne cikin wani rahoton da ya fitar game da farfadowar Afrika, sai dai ya ce, karuwar tattalin arzikin ya yi kasa da yanayin karuwar jama'a a kasashen, kuma hakan ya nuna bukatar ninka kokari wajen kara samar da ayyukan yi da kuma yaki da talauci a tsakanin al'umma.

Rahoton wanda aka kaddamar da shi a Nairobin kasar Kenya ya danganta matsalar rikicin kudi na duniya, da rashin kyakkyawan farashin kayayyakin da ake samarwa.

A cewar wannan rahoto, kididdigar shekara shekara game da yanayin tattalin arzikin na Afrika wanda bankin duniya ya gudanar, masu harkar fitar da albarkatun man fetur da dama a kasashen tsakiyar Afrika da hukumomin kula da al'amurran kudade na Afrika CEMAC, suna fuskantar wahalhalu game da sha'anin tattalin arzikin.

Rahoton ya ce, kasashen Najeriya, Afrika ta Kudu da Angola, sun kasance mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar, sun fara samun bunkasuwa bayan komadar tattalin arzikin da suka fada a shekarar 2016, amma farfadowar ba ta tafiya cikin sauri saboda rashin tsarin daidaita farashin kayayyaki da tsare tsare marasa tabbas.

Wasu alkaluma na baya bayan nan sun nuna cewa, kasashe 7 da suka hada da Cote d'Ivoire, Habasha, Kenya, Mali, Rwanda, Senegal da Tanzania, suna ci gaba da fuskantar sauyi game da sha'anin tattalin arzikinsu, inda suke samun karuwar kashi 5.4 cikin 100 daga shekarar 2015 zuwa ta 2017.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China