in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ba ta shirin shata-daga game da batun nukiliyar a zirin Korea
2017-04-18 13:15:56 cri
Fadar White House ta ce ba ta tsammanin Shugaban Amurka Donald Trump, zai shata-daga game da batun nukiliya a zirin Korea, ta na mai cewa, Amurka za ta ci gaba ta aiki da kasar Sin wajen warware matsalar.

Da yake ganawa da manema labarai, Kakakin fadar White House Sean Spicer, ya ce daukar irin wannan mataki bai taba aiki ba a baya.

Sai dai, Spicer ya bada misali da hari kan sansanin sojin saman Syria da Amurka ta kai a baya-bayan nan a matsayin wani gargadi dake nuna cewa Trump, zai iya daukar duk wani mataki da ya dace.

Sean Spicer ya kara da cewa, Amurka za ta yi aiki da kasar Sin game da batun na nukiliya a zirin Korea. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China