Tsohuwar firaministar kasar Australia Julia Gillard, ta yi kira da a dauki karin matakai na samar da ilimin bai daya ga 'ya'yan mata a yankin kudancin Saharar Afirka, a wani mataki na tabbatar da 'yan matan yankin sun samu ilimin firamare da na karamar sakandare yadda ya kamata.
Madam Julia Gillard wadda a yanzu haka ke jagorantar shirin hadin gwiwar kasa da kasa na raya ilimi, ta gabatar da wannan kira ne yayin wani taron ministocin kasashen duniya game da kudurin wanzar da ci gaba, wanda ya gudana jiya Laraba a helkwatar MDD.
Ta ce, bisa jadawalin da ake da shi, ba za a kai ga cimma burin samar da ilimi ga yara mata dake wannan yanki na Afirka ba, har sai nan da shekara ta 2111.
Game da batun kudurorin karni 17 masu alaka da wanzar da ci gaba, wadanda kuma ake fatan amincewa da su yayin taron MDD na watan Satumba, Gillard ta ce, hakan zai ba da damar kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, zuwa ga kara kwazo wajen ganin an samar da ilimi mai inganci, da dama ta ci gaba da samun ilimi ga kowa.
Sabbin kudurorin wanzar da ci gaba da aka yiwa lakabi da SDGs, sun kunshi harkokin kiyaye muhalli, da na bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin duniya, wadanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2016 da 2030. (Saminu)