A Litinin din da ta gabata, sakatare janar na MDD Ban Ki-moon, ya yi kira da kara yawan kayayyakin tallafin jin kai ga jama'ar dake cikin halin kunci a kasashen dake yankin babban tafkin nahiyar Afrika wadanda tashen tashen hankula ya daidaita.
Ban ya ce, ya damu matuka game da yadda ake take dokokin kasa da kasa da suka shafi ba da agaji a gabashin jamhuriyar demokaradiyyar Congo DRC da sauran sassan yankin.
Ban ya kara da cewar, batun tabarbarewar tsaro a Burundi shi ma wata babbar matsala, ya ce, a halin yanzu sama da mutane miliyan guda da suka hada da mutune 25,000 da suka rasa muhalli ne ke cikin matsanancin hali, kuma suna matukar bukatar tallafin gaggawa a kasar ta Burundi.
Domin kawo karshen wannan matsala, Ban, ya jaddada bukatar lalibo bakin zaren warware matsalar rikice rikice a yankin ta hanyar tuntubar tsoffin 'yan tada kayar baya a yankunan wadanda suka sha yin ikirarin ayyana samun galaba a yaki tsakanin su da hukumomi a yankin.(Ahmad Fagam)