Tasowar kasar Sin a matsayin wata babbar kasar tattalin arziki ya sa kaimi ga ci gaban tattalin arzikin Afrika ta hanyar baiwa nahiyar damar yawaita ayyukanta na zuba jari, in ji wani masanin kasar Kenya.
Zuba jarin kasar Sin na ci gaba da fadada a nahiyar Afrika, lamarin dake kasancewa alheri ga Afrika domin jimillar zuba jari ta karu, in ji babban manajan cibiyar yin nazari kan harkokin tattalin arzikin kasar Kenya (IAE), Kwame Owino, a yayin wani zaman taron Sin da Afrika na dandalin kasuwanci.
Haduwar ta yini guda ta tattara mahalartan da suka fito daga bangarorin daban daban domin bitar matsayin matsayin kasar Sin a cikin tattalin arzikin Afrika.
Mista Owino ya bayyana cewa, akwai wata huldar ci gaba tsakanin shigo da jarin kasar Sin a nahiyar Afrika da kuma karuwar kudin shiga a nahiyar.
A cewar cibiyar AIE, daya daga cikin manyan wadanda suka amfana da bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ita ce nahiyar Afrika.
Alkaluman gwamnatin Kenya sun nuna cewa, kasuwanci tsakanin Sin da Kenya ya karu da kashi 27 cikin 100 kowace shekara tsakanin shekarar 2011 da shekarar 2015. (Maman Ada)