Wani sabon rahoto da wata hukumar bincike mai zaman kanta a Afirka ta wallafa game da yadda al'ummar nahiyar Afirka ke kallon kasar Sin ya nuna cewa, kasar Sin tana da kima matuka a idon al'ummar Afirka fiye da kasar Amurka, sakamakon irin ayyukan raya kasa da Sin din ta ke gudanarwa a kasashen nahiyar.
Rahoton ya nuna cewa, hukumar ta gudanar da binciken nata ne a kasashe 36 na Afirka, inda mutane 54,000 suka bayyana ra'ayoyinsu game da yadda kasar Sin ta ke kara samun gindin zama a nahiyar ta Afirka.
Bugu da kari, rahoton binciken ya nuna cewa, kashi 24 cikin 100 na mutanen da aka zanta da su a kasashe 36 na Afirka, suna ganin cewa, kasar Sin ce ta biyu a fannin tsarin raya kasa, yayin da kasar Amurka ta ke kan gaba. Sai dai kuma wasu mutanen da aka zanta da su sun fi kaunar kasashen da suke yi musu mulkin mallaka ko kuma Afirka ta kudu a matsayin abin koyi.
Amma galibin wadanda aka zanta da su, suna kallon kasar Sin a matsayin kasar da ta ke tallafawa ci gaban kasashen Afirka.
Rahoton hukumar ya kara da cewa, a 'yan shekarun baya-bayan nan, kasar Sin tana kara zurfafa hadin gwiwa da kasashen Afirka, misali, dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) wanda aka kafa a shekarar 2000, wanda ya kasance wata muhimmiyar kafa ta kara kulla hulda da kasashen Afirka da ke yankin kudu da hamadar Sahara.(Ibrahim)