Kasar Sin ta kuduri aniyar gina sabbin filayen jiragen sama 136 nan da shekarar 2025.
Hukumar raya kasa da yin gyare-gyare ta kasar Sin da hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar sun bayyana cewa, wadannan filayen jiragen saman da ake fatan ginawa, za su kasance cibiyoyin zirga-zirgar fasinjojin da hajoji na kasa da kasa da shiyya-shiyya.
Tun a shekarar 2008 ne kasar Sin ta himmatu wajen gina filayen jiragen sama a sassan kasar daban-daban, lokacin da mahukuntan kasar suka fara zuba makuden kudade a bangaren sufurin jiragen sama, a wani mataki na magance matsalar kudin da duniya ta tsinci kanta a ciki.
Ko da yake ayyukan hidima sun inganta, amma filayen jiragen saman da kasar take da su a halin yanzu ba su wadatar ba, kuma suna warwatsa ne a wurare daban-daban na kasar.
Bayanai na nuna cewa, a karshen shekarar 2015 kasar Sin tana da filayen jiragen sama 207, tana kuma fatan za su kai 260 nan da shekarar 2020. Wasu alkaluma na cewa, a shekarar 2015, fasinjoji miliyan 910 ne suka tashi da kuma sauka a filayen jiragen saman kasar, ana kuma sa ran filayen jiragen saman za su biya bukatun fasinjoji biliyan 1.5 a shekarar 2020, sai kuma fasinjoji biliyan 2.2 a shekarar 2025.(Ibrahim)