An bukaci gwamnatocin kasashen Afrika su duba yiyuwar hada hannu da kamfanonin jiragen sama dake nahiyar, da nufin tabbatar da ingantaccen bangaren sufurin jiragen sama.
Kwararru mahalartar taro kan bangaren sufurin jiragen saman Afrika, sun bayyana cewa, galibin jiragen saman nahiyar ba su da kwarin kafa kamfanin jiragin sama na kashin kansu.
Da yake jawabi yayin taron, shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Nexus, Abdullahi Al-Sayed, ya ce samar da kamfanin na hadin gwiwa, zai taimaka wajen bunkasa bangeren sufurin jiragen saman nahiyar.
A nasa bangaren, Alan Peaford, shugaban kwamitin shirya taron, ya ce idan ya samu kyakkyawan tsari, bangaren sufurin jiragen saman na Afrika na da dimbin damarmaki da za su habaka tattalin arzikin nahiyar.
A cewar kungiyar kula da sufurin jiragen sama na kasa da kasa (IATA), nahiyar Afrika na shirin zama daya daga cikin wadanda bangaren sufurin jiragen samansu zai samu bunkasa cikin sauri nan da shekaru ashirin masu zuwa.
Taron na bana ya samu halartar wakilai dari biyar da hamsin daga kasashe hamsin da takwas, ciki har da wakilai daga kamfanonin jiragen sama dari daya da ashirin, da kamfanonin baje koli hamsin da shida. ( Fa'iza Mustapha)