Kasar Sin na shirin kashe kudade da yawan su ya kai kwatankwacin dalar Amurka biliyan 376 da miliyan 81, a sashen bunkasa harkokin sufuri, kamar dai yadda wasu alkaluma da ma'aikatar kula da sufurin kasar suka nuna.
Da yake karin haske yayin wani taron manema labarai game da hakan, ministan ma'aikatar ta sufuri Li Xiaopeng, ya ce cikin shirin ci gaban kasar na shekaru biyar biyar, wato tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, za a kashe kudi da yawan su ya kai Yuan Triliyan 15, a fannin raya ababen more rayuwa da suka jibanci sufuri, ciki hadda triliyan 3.5 da za a shigar sashen sufurin jiragen kasa, da tiriliyan 7.8 da za a kashe a fannin titunan mota, sai kuma Yuan biliyan 500 da za a kashe a fannin sufurin jiragen ruwa.
Mr. Li ya ce bayan kammalar wadannan ayyuka, Sin za ta kai ga tsawaita layin dogon ta da karin kilomita 30,000, inda kaso daya cikin uku zai zamo mai daukar jiragen kasa masu matukar sauri. Kaza lika titunan motar kasar za su karu da tsayin kilomita 320,000. Baya ga karin filayen jiragen sama 50 da za a gina domin daukar fasinja.(Saminu Alhassan)