Yayin tattaunawarsu, manyan jami'an bangarorin Sin da Burtaniya sun nuna yabo kan sakamakon da aka samu ta fuskar hadin gwiwar bangarorin 2, bayan an gudanar da taron shawarwari tsakaninsu a karon farko a watan Yuni na bara.
A yayin taron na wannan karo, jami'an bangarorin Sin da Burtaniya, sun yi musayar ra'ayi kan batutuwan da suka shafi yakar ta'addanci, da masu tsattsauran ra'ayi, da tabbatar da tsaron shafunan yanar gizo na Internet, da dakile gungun baragurbi masu aikata laifuka, da maganar tsaro a wurare daban daban dake janyo hankalin dukkan bangarorin 2.
Bisa tattaunawar da suka yi, manyan jami'an kasashen Sin da Burtaniya sun cimma daidaito, kan yadda za a gudanar da hadin kai tsakanin kasashen 2, musamman ma a fannonin tinkarar barazanar ta'addanci, da dakatar da yaduwar ra'ayin ta'addanci ta hanyar shafin yanar gizo, da tabbatar da tsaron zirga-zirgar jiragen sama masu dauke da fasinjoji, da dai makamantansu.(Bello Wang)