A wajen bikin na wannan karo, wasu kamfanoni 8 masu harhada makamai na kasar Sin, karkashin jagorancin hukumar masana'antun samar da makamai ta kasar Sin, sun kafa wata tawaga ta kasar Sin, don halartar bikin, inda suka yi amfani da hanyoyi daban daban, wajen nuna makaimai kirar kasar Sin, ciki hadda jiragen saman yaki, da makamai masu linzami, da motocin yaki, da jiragen ruwa na yaki, da jiragen sama marasa matuki, da na'urar bincike ta rada, da dai makamai masu inganci iri-iri.
Fadin wurin da kamfanonin kasar Sin suka kebe domin nuna kayayyakinsu ya kai muraba'in mita 1458, wanda ya zama mafi fadi a tarihin kasar Sin, a yayin halartar bikin nuna makamai da fasahohin tsaro na Abu Dhabi.
An fara gudanar da babban bikin nuna fasahohin zamani a fannin tsaro da makamai a Abu Dhabi ne tun daga shekarar 1993, daga bisani ake gudanar da bikin duk shekaru biyu-biyu. Zuwa yanzu, bikin ya riga ya zama irinsa mafi girma, kuma mafi tasiri a yammacin Asiya gami da arewacin nahiyar Afirka. Haka zalika, bikin ya kasance daya daga cikin manyan bukukuwan bajekolin makamai da fasahohin tsaro a duniya.(Bello Wang)