Manufar tsarin wanda ake fatan fara cin gajiyarsa cikin shekaru hudu masu zuwa, ita ce, fito da wani managarcin tsarin kula da lafiyar mutanen da suka manyanta.
Kamar yadda shirin ya kunsa wanda ma'aikatar kula da harkokin masana'antu da fasahar sadarwa ta zamani, da ma'aikatar kula da tsaron jama'a da hukumar lafiya da tsara iyalai ta kasar Sin suka tsara tare, nan zuwa shekarar 2020, kasar Sin za ta gina wuraren kula da tsofaffi na zamani wanda zai kunshi fitattun masana'antu sama da 100 baya ga wasu kamfanoni da suka shahara a duniya.
Bayanai na nuna cewa, nan da shekaru hudu masu zuwa, kasar Sin za ta gina cibiyoyin gwaji sama da 100 a wani mataki na kankamar wannan shiri.(Ibrahim)