Jami'in ya bayyana cewa, kasar Sin ta gabatar da rahotanni da dama ga tsarin sa ido kan magunguna na duniya. A matsayinta na kasar da ke kan gaba wajen samarwa da cinikin magungunan gargajiya a tsakanin kasa da kasa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen sa ido ga matsalolin da a kan gamu da su a sakamakon shan maganin gargajiya.
Mataimakin shugaban hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasar Sin Wu Zhen ya bayyana a gun taron cewa, kasar Sin ta kafa tsarin sa ido na kasa, da na larduna, da kuma na birane.
Game da matsalolin da ake fuskanta, Wu Zhen ya bayyana cewa, kasar Sin ta fara gudanar da aikin sa ido kan magunguna ne bayan sauran kasashen duniya, kuma tana fuskantar kalubale da dama a fannonin kimanta tsaro da hadarin magunguna. Kana yana fatan kasashen duniya za su kara yin hadin gwiwa da mu'amala a wannan fanni don tabbatar da tsaron magunguna tsakanin al'ummominsu tare da kiyaye lafiyar al'ummar duniya. (Zainab)