in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Har yanzu harkokin Cinikayyar kasar Sin a kasashen ketare na fuskantar kalubale
2017-02-15 10:50:26 cri
Wani jami'in ma'aikatar ciniki na kasar Sin, ya ce duk da ingantuwar al'amura da aka samu a watan Junairu, harkokin cinikayyar kasar a kasashen ketare na fuskantar kalubale.

Mataimakin Darakta Janar na sashen kula da harkokin ciniki a kasashen ketare na ma'aikatar ciniki ta kasar Sin, Wang Dongtang ya ce kalubalen da harkokin cinikayyar kasar ke fuskanta ba na gajeren zango bane.

Ya kuma bayyana matakan cinikayya masu tsauri da rashin bukatar kayyaki yadda ya kamata daga kasashen ketare da karuwar farashin sarrafa kayayyaki a matsayin kalubalen da harkokin cinikayyar kasar a ketare ka iya fuskanta nan gaba.

Sai dai, Wang ya ce har yanzu muhimman manufofin cinikayya da kasashen ketare ba su sauya ba, kuma kasar na amfana da su.

A bana harkokin kasuwacin kasar Sin sun farfado, inda aka samu ingantuwar harkokin fitarwa da shigar da kayayyaki. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China