Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yau Litinin a nan Beijing cewa, kasar Sin na adawa da matakin Koriya ta Arewa, na saba wa kudurin kwamitin sulhun MDD, inda ta harba makami mai linzami. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta yi kira ga sassa daban daban masu ruwa da tsaki da su kai zuciya nesa, a kokarin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan yanki.
Kalaman na Mr. Geng dai na zuwa ne bayan da Koriya ta arewan ta yi gwajin harba makami mai linzami mai cin matsakaici da kuma dogon zango a jiya Lahadi. (Tasallah Yuan)