A cikin wata sanarwa ta fadarsa, kwamitin sulhu ya nuna gamsuwa kan cigaban da aka samu a kasar Somaliya tun a shekarar 2012 tare da bayyana matakin hadin gwiwa na dandalin kasa na shugabannin Somaliya da su kara lokacin jawadalin zabukan 'yan majalisa har zuwa ranar 25 ga watan Oktoban shekarar 2016 kana zaben shugaban kasa har zuwa ranar 30 ga watan Oktoban shekarar 2016 domin ganin an aiwatar da muhimman matakai cikin tsarin wani shirin zabe da zai samu halartar kowa da kowa.
Yana da muhimmanci a rike yunkuri zuwa wani tsarin mulki na demokuradiyya bisa tsarin shirin zabe na gaskiya, sahihanci da kuma zai samu halartar kowa da kowa a shekarar 2016, da hakan zai taimaka yadda ya kamata wajen gudanar da zabukan wadanda za su samu halartar al'ummar kasa baki daya a shekarar 2020, in ji mambobi goma sha biyar na kwamitin.
Shirin zabe na yanzu na kasancewa wata dama ta tarihi na samarwa al'ummar Somaliya wani tsarin mulki da zai kara wakiltar al'ummar kasa da al'adunta da kuma addinanta, in ji kwamitin da kuma yake nuna yabo ga matakin dandalin kasa na shugabannin da ya maida hankali kan wakilcin kananan kabilu da al'ummar Banadir da kuma sanar da matakan baiwa mata kashi 30 cikin 100 na kujeru a zauren majalisun kasar. (Maman Ada)