in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Namibia ta yi ban kwana da kwararun Sin bayan shekaru 2 suna tallafawa kasar
2017-02-09 09:33:16 cri

A jiya Laraba ne mahukuntan kasar Namibia suka gudanar da bikin ban kwana da tawagar kwararru a fannin aikin gona na kasar Sin, bayan da suka kammala aikin tallafi na tsawon shekaru 2 a kasar.

Kwararrun su 15 sun gudanar da ayyuka a fannin raya noman rani, da harkar kula da lafiyar dabbobi, da kuma inganta cibiyoyin bincike, karkashin wani shiri mai lakabin SSC, na hadin gwiwa tsakanin Namibia, da kasar Sin, tare da hukumar abinci da aikin gona ta MDD FAO.

Yayin taron na ban kwana da kwararrun kasar Sin, mukaddashin jakadan kasar Sin a Namibia Li Na, ya ce cikin shekaru biyu da suka gabata, masu ruwa da tsaki a wannan shiri sun samar da kyakkyawan yanayi da kayayyakin aiki masu inganci, domin baiwa kwararrun na kasar Sin damar gudanar da aikin su yadda ya kamata.

Shi ma wakilin hukumar FAO Babagana Ahmadu, ya bayyana cewa, shirin SSC a Namibia, ya cimma cikakkiyar nasara, wajen tallafawa yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na bunkasa harkar noma.

Da yake karin haske game da shirin, ministan ma'aikatar gona, ruwa da gandun dajin kasar ta Namibia John Mutorwa, ya ce an fara aiwatar da shirin ne cikin watan Yunin shekara ta 2014, kuma ana sa ran kammalar sa a ranar 30 ga watan Afirilun wannan shekara.

Mr. Mutorwa ya ce, ma'aikatar sa ta gudanar da taron tattauna halin da ake ciki game da shirin, tare da wakilan hukumar FAO, da na ofishin jakadancin kasar Sin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China