in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kudaden Sin yuan za su bunkasa tattalin arzikin Namibiya
2015-09-14 09:54:29 cri

Wani babban kwararre mai bincike kuma manajan banki a kasar Namibiya Namene Kalili, ya ce, bullo da yin hada hada kasuwanci da kudaden kasar Sin wato yuan zai iya habaka tattalin arzikin kasar ta Namibiya.

Bankin Rand Merchant na kasar Namibia wanda ke hulda da babban bankin kasar wato National Bank of Namibia, shi ne ya kaddamar da fara amfani da kudaden na yuan a ranar Alhamis din nan domin saukaka gudanar da hada hadar cinikayya ta kasa da kasa.

Kalili ya ce, a bara huldar kasuwanci tsakanin kasar Sin da Namibiya ta kai dala biliyan 5 da digo 6, sannan ya kara da cewar, ana sa ran tattalin arzikin kasar Namibiyan zai yi matukar bunkasa sakamakon yadda kasar ta dukufa wajen inganta samar da ababan more rayuwa, wanda hakan zai iya kara yawan adadin kayayyakin da kasar ke samarwa.

Ya ce, musamman yadda kasar ta fi mai da hankali wajen inganta hanyoyin sufuri da wutar lantarki da kuma bangaren sufuri ta ruwa zai matukar aza kasar kan kyakkyawar turba a wannan shiyya.

Kalili ya kara da cewar, zuba jarin da kasar ta yi a wadannan fannoni zai taimaka mata wajen karfafa dangantaka tsakaninta da kasashe na kudancin Afrika da kuma yankin Asiya.

Ya kara da cewar, sakamakon yadda kasar Sin ke sayarwa kasar Namibiya kayayyakin da masana'antu ke amfani da su, hakan zai matukar bunkasa ci gaban masana'antun kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China