in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarin da Sin ta zuba a Namibiya ya kai dalar Amurka biliyan 4.6
2015-03-16 10:23:49 cri

A kasar Namibiya, ana samun kamfanonin kasar Sin fiye da 40 wadanda suka zuba jarin na kusan dalar Amurka biliyan 4.6 da samar da ayyukan yi ga mutanen Namibiya fiye da dubu shida, a cewar jakadan kasar Sin da ke Namibiya, mista Xin Shunkang.

A yanzu haka, darajar jarin da kamfanonin kasar Sin a Namibiya ta cimma dalar Amurka biliyan uku, in ji mista Xin.

Sin da Namibiya sun sanya hannu kan yarjejeniyar zuba jari da ba da kariya a cikin watan Agustan shekarar 2005, a yayin da wata dokar da ta shafi zuba jarin waje da za a bayyana a gaban 'yan majalisar dokokin kasar.

Mista Xin ya tabbatar da cewa, ofishin jakadancin kasar Sin na ba da kwarin gwiwa ga kamfanonin kasar Sin da su kara zuba jarinsu a kasar Namibiya, da zurfafa dangantaka tsakanin kamfanonin cikin gida da su daukar ma'aikatan wurin.

Ofishin jakadancin kasar Sin ya dauki niyyar bunkasa kwarewa, musammun ma tsakanin matasa, ta hanyar shirya tarurukan kara wa juna sani a fannin kiwon lafiya, noma, sadarwa da sauransu.

Yan Namibiya sun samu damar zuwa kasar Sin tare ta hanyar samun kudin karatu da ma'aikatar ilimi ta Namibiya ke ba da wa. Bisa tsarin musanyar kwararru, kasar Sin ta taimaka wa kasar gina wata cibiyar horar da matasan Namibiya a Grootfontein, wani birnin dake da tazarar kilomita 460 da hedkwatar Windhoek.

Jarin da kasar Sin ta zuba a Namibiya ya karu zuwa dalar Amurka miliyan 179 a shekarar 2011 da 2012, kuma ya cimma dalar Amurka biliyan 3,9 a shekarar 2013. Kuma muhimman ayyukan zuba jarin sun fi shafar bangarorin ma'adinai da kere kere. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China