Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi kira a ranar Laraba ga ma'aikatan kiwon lafiya dake yajin aiki a cikin asibitocin kasar da su koma wuraren aikinsu, da kuma ba da dama ga ci gaban tattaunawa tare da gwamnati kan albashinsu.
Shugaban Kenyatta ya nuna damuwa cewa, kusan marasa lafiya 20 suka mutu tun farkon fara yajin aikin. Likitoci da ma'aikatan jinya sun dakatar da aiki a ranar Litinin, tare da bukatar ganin an aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2013 tare da gwamnatin kasar, dake tsokaci kan wani karin albashi da kashi 300 cikin 100. (Maman Ada)