Dangane da lamarin, babban sakataren yarjejeniyar cinikin duniya ta dabbobin daji da tsire-tsire dake bakin karewa ta CITES John E.Scanlon ya bayyana a jiya cewa, matakin da kasar Sin ta dauka ya sa kaimi matuka ga kasa da kasa, lamarin ya ba da gudummawa sosai wajen karfafa aniyar gamayyar kasa da kasa wajen tsayar da cinikin hauren giwa ba bisa doka ba.
Bugu da kari, ya ce, harkar din ta nuna babbar aniyar kasar Sin na kin nuna sassauci ko kadan kan irin wannan ciniki ba bisa doka ba, ba kawai ya nuna cewa, a halin yanzu, kasar Sin na karfafa dokoki da kuma aiwatar da dokokinta kan cafke hauren giwa na cinikin ba bisa doka ba, haka kuma, lamarin zai inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen dake da giwaye, kasashen da ake jigilar hauren giwa da kuma kasashen da ake sayar da hauren giwa, domin hana cinikin hauren giwa da sauran dabbobin daji da tsire-tsire na ba bisa doka ba. (Maryam)