Wani babban dan majalisar kasar Kenya ya ce, aikin gina hanyar jirgin kasan da Sin ke gudanarwa a Kenya wanda zai hade birnin Mombasa zuwa Nairobi babban birnin kasar, zai yi matukar habaka cigaban tattalin arzikin kasar.
Adan Duale wanda kuma shi ne shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin kasar ta Kenya ya furta hakan ne cikin wani sharhi da ya gabatar wanda wata mujalla ta wallafa, ya ce aikin gina layin dogon tamkar wani mataki ne na farfado da cigaban kayayyakin more rayuwa a kasar.
Duale ya kara da cewar, aikin layin dogon zai bunkasa cigaban tattalin arzikin kasar ta fuskoki da dama, musamman wajen samar da sabbin hanyoyin bunkasuwar kasuwanci ga kasar.
Ya ce fannin aikin gona da masana'antu ne za su fi cin gajiyar aikin gina layin dogon.
Kasar Kenya tana hasashen samun bunkasuwar cinikayya da makwabtan kasashe da zarar aikin ya kammala.
Duale ya ce, baya ga rage cunkuso da aikin zai yi a tashar ruwan Mombasa, aikin gina layin dogon zai taimaka wajen zirga zirgar kwararru a kasashen dake makwabtaka da kasar.(Ahmad Fagam)