A cewar Madam Hua, hakika wasu gidajen dabbobi dake biranen Shanghai, Beijing, da Hangzhou na kasar Sin sun sayi wasu giwaye 35 daga hannun mahukuntan kasar Zimbabwe, a kwanakin baya. Kuma an biya mahukuntan kasar Zimbabwe kudin, wadanda za a yi amfani da su wajen samar da kariya ga namun dajin kasar.
Kakakin kasar Sin ta nanata cewa, wannan batun ne na kasuwanci, kuma ya dace da yarjeniyoyin kasa da kasa da dokokin kasashen Sin da Zimbabwe. Don haka labarin da wasu kafofin watsa labaru suka watsa ba shi da tushe, kuma an tsara shi ne bisa buri maras kyau.
Jami'ar ta ce wasu gidajen dabbobi a wasu wurare daban daban na duniya, sun saba irin wannan aiki na shigo da namun daji daga ketare. (Bello Wang)