Sai dai wani dan kasar Sin da ya sa hannun batun ya bayyana cewa, wannan labarin ba gaskiya ba ne.
Dangane da wannan batu, Madam Song Li wadda ta kafa asusun kare namun daji tsakanin kasar Sin da kasar Zimbabwe ta bayyana cewa, wadannan giwaye 35 namun daji da gidajen namun dajin Shanghai da na Beijing da gidan namun dajin Hangzhou suka saya ne daga kasar Zimbabwe, masu cinikin dabbobi na kasar Sin da hukumar kula da harkokin lambun shan iska na kasar Zimbabwe sun kuma kulla yarjejeniya kan wannan ciniki a hukunce.
Sa'an nan, wandannan gidajen naman daji sun biya hukumar kula da namun daji ta kasar Zimbabwe da kuma lambun shan iska na Zimbabwe kudi kai tsaye.
Bugu da kari, wadannan gidajen namun daji na kasar Sin sun sayi giwaye guda 35 ne daga kasar Zimbabwe, ba kamar yadda kafofin watsa labarai na kasashen ketare suke yayatawa, wai an baiwa kasar Sin 'ya'yan giwaye guda 35, zakoki guda 8, kuraye guda 12 da kuma rakumin dawa guda daya ba. (Maryam)