Wani jami'in gwamnati a kasar Somalia, ya tabbatar da kisan da mayakan kungiyar Al-Shabaab suka yi wa wani sojin kasar, inda suka harbe shi, a garin Bosaso na jihar Puntland.
Shugaban kotun koli na sojin Puntland Abdifitah Haji Aden, ya ce an harbe Abdikarim Hassan Firdhiye ne lokacin da ya fito daga wani gidan radio, inda aka yi hira da shi kan wasu batutuwa dake gaban kotu.
Tuni dai kungiyar ta Al-Shabaab, ta dauki nauyin kisan.
A nasu bangare, jami'an tsaro a Puntland sun daura damarar farautar mayakan, al'amarin da ya kai ga sanya dokar takaita zirga-zirga a garin na Bosaso.
Abdikarim Firdhiye shi ne babban jami'i na uku da mayakan Al-Shabaab suka kashe cikin makonni biyu da suka gabata.
Kungiyar Al-Shabaab dai ta kai hare-hare da dama babu kakkautawa, a Somalia, a yakin da ta shafe shekaru goma tana yi da gwamnatin kasar.
(Fa'iza Mustapha)




