Manyan jami'an sojojin tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afrika AU dake Somaliya (AMISOM) sun fara wani zaman taro a ranar Litinin a Mogadishu domin yin nazari da kimanta ayyukansu, da kuma dabarunsu na yaki da ta'addanci.
Wannan taron komandojin bangaren AMISOM ya mai da hankali kan karfi da kwarewar rundunoni a filin daga da kuma yiyuwar kara yawan dakaru, ta yadda za a baiwa tawagar zarafin gudanar da ayyukanta na kai samame yadda ya kamata, da karbe yankunan dake hannun kungiyar Al-Shabaab.
A cikin jawabinsa na bude taron, wakilin musamman na shugabar kwamitin kungiyar tarayyar Afrika AU kan Somaliya, mista Francisco Caetano Madeira, ya nuna yabo ga dakarun AMISOM kan jajircewarsu wajen tabbatar da tsaron aikin zabe aka gudana ba tare da matsala ba.
Haka kuma ya jaddada bukatar gaggawa ta karfafa karfin rundunar sojojin Somaliya, wanda ya kasance muhimmin mataki domin dabarar janyewar AMISOM daga kasar, in ji jami'in. Komandojin bangaren AMISOM za su sadu da takwarorinsu na kasar domin gabatar da bayanai kan ayyukansu na hadin gwiwa da sauransu. (Maman Ada)




