Kwanciyar hankali ya sake dawowa a birnin Galkayo, dake tsakiyar kasar Somaliya, inda wani kazamin fada ya barke tsakanin dakaru masu gaba da juna, wanda ya janyo mutuwar mutane fiye 45 da gudun hijirar mutane dubu 90 tun farkon watan Oktoba, a cewar cibiyar MDD dake kula da harkokin jin kai (OCHA). (Maman Ada)




