Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya kaddamar da wani shiri na sulhu, tare da hada kan 'yan kasar sa, a wani mataki na kawo karshen rarrabuwar kawunan kabilun kasar, da dakile tashe tashen hankula dake addabar jaririyar kasar.
Da yake kaddamar da shirin a jiya Laraba, Mr. Kiir ya shaidawa majalissar dake kula da sha'anin mulkin rikon kwaryar kasar cewa, manufar shirin ita ce baiwa al'ummun kasar damar kawo karshen zub da jinni, tare da daukar matakan kare kasar daga daidaicewa.
Ya ce, yana fatan al'ummar kasar za su yafi juna, su kuma yafe masa duk wani kuskure da ya aikata a matsayin sa na jagoran kasar. Kaza lika yana da burin ganin 'yan kasar sun rungumi juna a matsayin 'yan uwa dake da martaba, ba tare da nuna wani banbanci ba.
Shugaban Kiir ya kara da cewa, za a kafa wani kwamitin dattawan kasar, wanda zai kunshi masana, da jagororin al'umma, da malaman addinai, wadanda za su taimaka wajen cimma nasarar aiwatar da manufofin wannan shiri a dukkanin matakai na yankunan kasar baki daya.(Saminu)