Kasashen Sudan ta Kudu da Uganda sun dauki niyyar kafa wata tashar bincike a kan iyakarsu guda domin rage tsawon lokacin tafiye tafiye, da kuma saukaka kasuwancin kan iyaka, in ji wani jami'i a ranar Litinin.
Joseph Ayok Anei, karamin sakatare a ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta Kudu, ya bayyana a ranar Litinin cewa, an cimma wata yarjejeniya a Kampala, babban birnin Uganda a makon da ya gabata domin karfafa kasuwanci, tare da saukaka shige da ficen kayayyaki, jama'a da wasu hidimomi tsakanin kasashen biyu.
A cewarsa, da zaran an gina, tashar kan iyakan za ta rage adadin tsaiko a cikin kasuwancin kan iyaka da sauran hidimomi da hada ayyukan bincike a kan iyakoki a wuri guda daga kowane bangare.
Tashar ta hadin gwiwa za ta saukaka shige da ficen mutane da kayayyaki, tare da rage lokacin da ake kwashewa a cibiyoyin bincike na shiga. Da zaran masana'antu sun fara aiki a Sudan ta Kudu, wannan zai kasance wani abun moriyar juna, in ji mista Anei a gaban 'yan jarida a Juba, babban birnin Sudan ta Kudu.
A cewar yarjejeniyar, kasashen biyu za su kafa yankunan sanya ido na hadin gwiwa domin saukaka shige da ficen kayayyaki da mutane a cibiyoyin shiga.
Uganda ta kasance mihimmiyar abokiyar kasuwanci ta Sudan ta Kudu a shiyyar gabashin Afrika. Kayayyakin da Uganda take fitarwa zuwa makwabciyarta ta arewa sun cimma dalar Amurka biliyan 1,18 tun daga shekarar 2008, a cewar wasu alkaluman ma'aikatar kasuwancin Uganda. (Maman Ada)