Mista Lu Kang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta ba da tallafin kudi ga aikin wanzar da zaman lafiya a Somaliya da kungiyar kasashen Afirka AU ke gudanarwa. A cewar jami'in, matakin da kasar Sin ta dauka ya nuna yadda kasar take goyon bayan kokarin jama'ar kasashen Afirka na ganin a daidaita al'amuran nahiyar Afirka bisa dabara irin ta Afirka. Haka zalika, jami'in ya ce kasar Sin na son ci gaba da tallafawa aikin wanzar da zaman lafiya a sauran sassan nahiyar Afirka a nan gaba.
Rahotanni na cewa, yawan kudin da kasar Sin ta samar wa kungiyar AU a kwanakin baya don aiwatar da aikin kiyaye zaman lafiya a Somaliya ya kai dalar Amurka miliyan 1.2.(Bello Wang)