Wani babban jami'in sojin kasar ta Somali, wanda ya kammala taron tattaunawa na kwanaki 3 a Mogadishu, ya ce za su yi aiki tukuru domin tabbatar da kwato yankunan dake karkashin ikon mayakan Al-Shabaab.
Kungiyar tarayyar Afrika ta fada cikin wata sanarwa da ta fitar a Mogadishu cewa, manyan kwamandojin sojin zasu hadu domin kammala shirye shiryen da suka dace don fara aikin.
Sanarwar ta kara da cewa, daga cikin muhimman batutuwan da suka tattauna a loakcin taron na kwanaki 3, sun hada da yadda za'a karfafa rundunar sojin ta SNA, a daidai lokacin da AMISOM ke shirye shiryen kawo karshen wa'adin aikinta a kasar Somali a shekarar 2018.
Daga cikin dabarun janye dakarun aikin wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afrikar, kwamitin tsaron na AMISOM ya bukaci a fara janyen dakarun dubu 22, ciki har da na Kenya a farkon watan Oktoba na shekarar 2018, kuma a kammala janyensu zuwa karshen shekarar 2020.(Ahmad Fagam)