Kasar Sudan ta Kudu ta bayyana a ranar Litinin cewa, Kenya da Habasha, kasashe ne makwabtaka na gabashin nahiyar Afrika, kuma sun taimaka matuka wajen kulla yarjejeniyar zaman lafiya da aka sanya wa hannu domin kawo karshen rikicin da Sudan ta Kudu ke fama da shi a cikin shekaru biyu.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta Kudu, mista Mawien Makol Arik, ya bayyana a birnin Juba, cewa ziyarar faraministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn a ranar 28 ga watan Oktoba, da muhimmiyar rawar da kasar Kenya ta taka a cikin kokarin gina zaman lafiya da kuma goyon bayan gina ayyukan kare fararen hula, sun kasance muhimman abubuwa wajen kafa huldar danganataka mai karfi tare da wadannan kasashe. (Maman Ada)