Da yammacin jiya Laraba, shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya fito a bainar jama'a domin ya kwantar da hankalin 'yan kasar bayan rade radin da ake yi na cewa ya mutu, lamarin da ke neman tada hankula a kasar, da ma makwabtata.
Shugaba Kiir, wanda ke cikin wata mota kirar fikof ya kewaya birnin Juba har sau 3 a gaban dandazon magoya bayansa.
Ya shedawa 'yan jaridu cewa, makiyansa ne ke baza jita jitar cewa ya mutu.
An dai fara rade radi game da mutuwar shugaban ne, tun a ranar Talatar da ta gabata har zuwa Laraba, lamarin da ya haddasa wasu 'yan kasuwa da kungiyoyi dakatar da harkokinsu na yau da kullum.(Ahmad Fagam)