in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNWTO: Masar ce ke kan gaba a fannin yawon bude ido
2016-11-01 10:59:40 cri

Babban sakataren hukumar lura da yawon shakatawa ta MDD UNWTO Taleb Rifai, ya bayyana kasar Masar a matsayin kasar dake sahun gaba, wajen cin gajiyar harkokin yawon bude ido, yana mai cewa, akwai alamu dake nuna tabbatar kasar a wannan matsayi.

Mr. Rifai wanda ke bayyana hakan yayin taro na 104, na manyan jami'an hukumar ta UNWTO da ya gudana a birnin Luxor na kasar ta Masar, ya kara da cewa, yawan mahalarta taron na wannan karo, ya dada tabbatar da imanin da al'ummun duniya ke da shi game da sashen yawon bude ido na kasar Masar.

A farkon wannan shekara ne UNWTOn ta ayyana birnin Luxor a matsayin "Cibiyar yawon bude ido ta duniya ta bana", kuma taron na yini 2 dake gudana a birnin, ya samu halartar wakilai kimanin 170 daga kasashen duniya 40.

An bude taron ne a jiya Litinin, ana kuma fatan mahalartan sa za su mai da hankali kan muhimman batutuwa 3 dake suhun gaba a ajandar hukumar UNTWOn, tsakanin shekarar da muke ciki zuwa shekara ta 2017 mai zuwa.

Batutuwan kuwa su ne harkar tsaron matafiya, da tasirin ci gaban fasahohi ga harkar yawon bude ido, tare kuma da tabbatar da dorewar ci gaban da ake samu a fannin na yawon shakatawa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China