in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sha'anin yawon shakatawa na kasar Sin ya samu bunkasuwa sosai
2016-08-15 14:05:51 cri

Sakamakon bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na kasar Sin a 'yan shekarun nan, ya sa Sinawa su kai ziyara a wurare daban-daban a duniya, hakan ba kawai ya taimaka ga bunkasuwar tattalin arzrikin al'umma ba, har ma ya nuna wa duniya kyakkyawar surar kasar Sin ta bude kofarta ga kasashen waje, da kuma sa kaimi kan yin mu'ammala tsakanin jama'ar Sin da al'ummomin duniya baki daya.

Alkaluman hukumar yawon shakawata ta kasar Sin sun nuna cewa, kasuwar yawon shakatawa ta bunkasa sosai a kasar Sin a watanni shida na farkon shekarar bana, yawan Sinawa da suka kai ziyarar yawon shakatawa a kasar ya kai biliyan 2.236, wanda ya karu da kashi 10.47 cikin dari bisa na makamancin lokaci na bara, kuma yawan wadanda suka kai ziyara a kasashen waje ya kai miliyan 127, wanda ya karu da kashi 4.1 cikin dari. Yawan kudin da Sin ta samu a wannan fanni ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 2250, wanda ya karu da kashi 12.4 bisa dari. Yawan ababen da ake gina a fannin yawon shakatawa a nan kasar Sin ya kai 9944, inda yawan kudin da aka zuba ya kai RMB yuan biliyan 421.15, wanda ya karu da kashi 30 cikin dari.

Rahoton kuma ya yi hasashen cewa, a wannan shekara, yawan Sinawa da suka kai ziyara a kasashen waje da kuma kudin da suka kashe ta fuskar yawon shakatawa za su sake kai matsayin farko a duniya. Kana kuma kasar Sin ta kasance wadda ta fi ko wace kasa son kai ziyara a cikin kasarsu, ciki hadda kasashen Thailand, Japan, Korea ta kudu, Vietnam, Rasha, Maldives, Birtaniya da dai sauransu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China