Kasar Rwanda tana shirin bunkasa muhimmin tattalin arzikinta na yawon bude ido a yayin daya daga cikin manyan tarukan kasa da kasa kan yawon bude ido, da zai gudana a wata mai zuwa a birnin Kigali, babban birnin kasar.
Wannan karamar kasa dake tsakiyar nahiyar Afrika za ta karbi bakuncin taron shekara shekara karo na 41 kan yawon bude ido na duniya daga ranar 14 zuwa 17 ga watan Nuwamba, tare da burin kara bunkasa bangaren yawon shakatawa da matsayin wani ginshikin ci gaban tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi a nahiyar, tare da taimakon tsare tsaren tattalin arziki na kirkire kirkire, da na sabbin fasahohin zamani da kuma hadin gwiwa. (Maman Ada)