Haka zalika ya ce, ficewar Burtaniya daga kungiyar tarayyar kasashen Turai ta kasance wani babban kalubale ga dunkulewar kasa da kasa baki daya, amma, yana imanin cewa, tabbas ne kasashen duniya za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a nan gaba, kuma wadannan mahalarta taron dake son kafa kamfanonin kansu za su samar da dama mai kyau wajen raya hadin gwiwar kasa da kasa.
Bugu da kari, Mr. Obama ya ce, tun da aka bullo da taron kafa kamfanonin kasa da kasa a shekarar 2009, ya tattauna da masu kafa kamfanoni da dama, ya gane wahalar da suka sha sosai a wannan fanni, shi ya sa, yana fatan gwamnatoci da kamfanonin kasa da kasa, har ma da gamayyar kasa da kasa baki daya za su iya samar wa matasa wandanda suke son kafa kamfanoni taimako yadda ya kamata, ta yadda za a iya kyautata yanayin tattalin arzikin duniya cikin hadin gwiwa.
Masu kamfanoni, masu zuba jari da kuma matasa masu son kafa kamfanoni sama da dubu daya da suka zo daga kasashe kimanin 170 sun halarci taron da aka yi a Silicon Valley na kasar Amurka, kuma taron na shekara mai zuwa, za a yi shi a kasar India. (Maryam)