in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta bukaci Sudan ta kudu da ta kawar da kungiyoyin masu dauke da makamai
2016-08-30 10:51:58 cri

Cibiyar yada labarai ta SMC ta rawaito cewa, gwamnatin Sudan ta bukaci makwabciyarta Sudan ta kudu da ta gaggauta cika alkawarin da ta dauka na fatattakar kungiyoyi masu dauke da makamai.

SMC ta jiyo ministan yada labaran kasar Sudan Ahmed Bilal Osman, ya furta cewa, Sudan tana jiran Sudan ta kudu ta cika alkawarin da ta dauka, inda mataimakin shugaban kasar Taban Deng ya ayyana cewa, za'a kawo karshen kai komo na kungiyoyi masu dauke da makamai a Juba cikin kwanaki 24.

Osman ya ce, yana fatan Sudan ta kudun za ta cika wannan alkawarin da ta dauka kafin cikar wa'adin da gwamnatin ta dauka.

Sannan ya yaba da irin kyakkyawar fahimta dake tsakanin kasashen biyu, ya kara da cewa, "Muna kokarin tabbatar da hadin kan Sudan ta kudu, kuma muna tallafawa kokarin MDD na samar da kwanciyar hankali a jaririyar kasar".

Shi dai Taban Deng, ya ambata a lokacin ziyarar aiki da ya kai kasar Sudan a ranar 22 ga wannan wata cewa, ba za su yarda kasar ta kasance a matsayin wata maboya ga masu dauke da makamai ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China