in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 14 sun mutu a harin da aka kai a wani masallacin Kabul
2016-10-12 10:24:18 cri

A kalla mutane 14 suka mutu yayin da wasu fiye da 40 suka jikkata a ranar Talata da yamma a cikin wani harin da wasu mutane dauke da makamai suka kai a wani masallacin dake Kabul, babban birnin Afghanistan, inda daruruwan mabiya darikar Shi'a suke bikin Ashura, daya daga cikin manyan bukukuwa bisa ga kalandar 'yan Shi'a.

A cewar bayanin farko, mabiya Shi'a 14 suka mutu, kana fiye da 40 suka jikkata a cikin harin ta'addancin kan masallacin Ziarrat-e-Shakhi dake yammacin Kabul.

Adadin wadanda suka mutu zai iya karuwa domin yawancin wadanda suka jikkata suna cikin wani hali mai tsanani, in ji wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaya sunanta.

Wasu ganau sun tabbatar da cewa, sun ji karar fashewar gurmeti sau uku da kuma harbe harbe da misalin karfe 7 da minti 50 na yamma bisa agogon wurin a cikin masallacin, dake kusa da jami'ar Kabul dake unguwar Jamal Mina. Kuma yawancin mutanen da suka mutu mabiya Shi'a ne.

Daga cikin wadanda suka mutu, akwai wani 'dan sanda, kuma saura 'yan sanda uku na daga cikin wadanda suka jikkata, in ji wannan majiya.

Bikin Ashura zai gudana ranar yau Laraba domin tunawa da mutuwar Liman Hussein, jikan Manzon Allah, Annabi Mohammed (SAW), da aka kashe a shekarar 680. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China