in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da harin kunar bakin wake da aka kai a Afghanistan
2014-03-19 11:57:05 cri

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya a ranar Talata ya yi tir da harin kunar bakin wake na bam da aka kai a safiyar Talata a arewa maso yammacin kasar, a inda kwamitin ya ce wannan hari ne na ta'addanci. Wakili na din-din-din na kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya, wanda ke wakiltar Luxemburg, Sylvie Lucas, wanda a yanzu shi ne shugaban kwamitin tsaron na karba-karba a wannan watan, ya fada a cikin wata sanarwa cewar, yayan kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniya sun yi kakkausar suka a game da harin ta'addanci da aka kai a lardin Faryab dake Afghanistan, a ranar 18 ga watan Maris. Kamar yadda sanarwar ta bayyana, shugaban ya ce, harin ya haddasa asarar rayuka da dama, tare da raunata fararen hula wadanda ba su san kome ba a kan harin.

Sanarwar ta kara da cewar, mambobin kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniyar suna jimamin wannan rashin tare da mika ta'aziyyarsu ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma jama'a da gwamnatin Afghanistan, tare da fatan wadanda suka jikkata za su samu sauki a cikin gaggawa.

Sanarwar ta kwamitin tsaron na majalisar dinkin duniyar ta nuna tsananin damuwa a game da barazanar kungiyoin Taliban da na al-Qaida da kuma kungiyoyin dake dauke da makamai suke haddasawa ga jama'a da kuma rundunar tsaro ta kasar Afghanistan da dakarun kasashen ketare, da kuma yin barazana ga hobbasa na agaji da kasashen waje ke baiwa ga kasar ta Afghanistan.

Kwamitin tsaron na majalisar ta dinkin duniya mai mambobi 15, ta jaddada bukatar da ke akwai na ganin an dauki mataki na shari'a a kan wadanda ke aiwatar tare da shirya hare-haren, da kuma masu ba su kudi suna aiwatar da ta'addanci, a inda kuma aka bukaci dukanin kasashe da su goyi bayan hukumomin kasar Afghanistan a yakin da take yi da ta'addanci. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China