in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hari kan asibitin Afghanistan kuskure ne, in ji komandan Amurka
2015-11-26 10:42:24 cri

Babban komandan dakarun Amurka dake kasar Afghanistan, John Campbell ya bayyana a ranar Laraba cewa, kazamin harin da jirgin yakin Amurka da ya shafi wani asibitin Afghanistan a watan da ya gabata, ya kasance a matsayin wani kuskure na dan adam, tare da kuma amince cewa, wasu mambobin tawagar sojojin Amurka dake da hannu kan wannan lamari ba su girmama dokokin aikinsu ba.

Asibitin ya sha luguden wuta na jirgin yakin Amurka bisa kuskure a lokacin da aka yi tsammanin wani gini ne na daban, mai nisan daruruwa mita inda wasu majiyoyi suka bayyana cewa, akwai mayaka wurin, in ji komandan Campbell a Pentagone a yayin wani taron manema labarai kan Afghanistan.

Jirgin yakin Amurka samfurin AC-130 ya lalata a ranar 3 Oktoba wani asibitin dake karkashin wata kungiyar ba da agaji da ake kira MSF, tare da kashe ma'aikatan asibitin 12 da masu jinya 10, da kuma raunana majinyata kusan talatin. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China