A cikin jawabinta a yayin bikin ba da lambobin yabon, wakiliyar hukumar UNESCO dake kasar Sin Marielza Oliveria ta bayyana cewa, tun daga shekarar 2000, zuwa yanzu, an samu ci gaba sosai a harkokin yaki da jahilci a duniya. Amma duk da wannan nasara, ana fuskantar kalubaloli masu yawa. A halin yanzu, akwai baligai kimanin miliyan 781 da ba su iya karatu ko rubutu ba, kuma kimanin kashi 2 bisa 3 daga cikinsu mata ne, don haka, ya zama wajibi a daidaita wannan matsala.
Haka zalika, Marielza Oliveria ta ce, a halin yanzu, kasashen duniya sun fara aiwatar da jadawalin neman dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030, inda suka dukufa wajen cimma wannan buri cikin shekaru 15 masu zuwa, watau samar da ilmi ga al'ummominsu har tsawon rayuwarsu. Haka kuma, inganta harkokin yaki da jahilci ya kasance abu mai muhimminci a wannan jadawali. Muddin ana bukatar samun dauwamammen ci gaba a nan duniya, wajibi a tabbatar da cewa, ko wane mutum a duniya ya iya karatu da rubutu. (Maryam)