Kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakani daga barnatarwar kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ya zama wani batun da aka dora muhimmanci sosai a kai. A gun bikin bude taron, babbar direktar kungiyar UNESCO Irina Bokova ta ce, bata abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni wani bangare ne na tashin rikicin da ya shafi jin kai, kuma wannan na da nasaba da aikin kare rayuwar dan Adam.
A gun bikin bude taron, shugaban taron kungiyar UNESCO karo na 37 kuma mataimakin ministan ilmi na Sin Hao Ping ya yi jawabin cewa, bala'u daga indallahi da yadda ake lalata abubuwa sun kawo babban kalubale ga aikin kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni, sannan hare-haren ta'addanci da aka kaiwa a kasashen Tunisiya, Faransa, Kuwaitt, sun sake nuna muhimmancin al'adu da sa kaimi ga samar da zaman lafiya da jituwa a duniya.(Bako)