Bisa kiyashin shekarun miliyan 3,5, wadannan sauran kasusuwa na Australopithecus afarensis an gano su a kasar Tanzaniya da Habasha.
Masanan Kenya sun bayyana cewa aikin bincike na shekaru hudu da gwaje gwajen kimiyya sun taimaka wajen gano wadannan sauran kasusuwa na halitar dan adam na farko.
Dokta Emma Mbua, mai bincike ta hadin gwiwa da gidan tarihin kasa na Kenya, ta bayyana cewa wannan gano wadannan sauran kasusuwan Australopithecus afarensis na kasancewa wani muhimmin mataki na bangaren binciken burkushin halittu.
"Yanzu muna da shaidun kimiyya dake tabbatar da cewa Kenya ta kasance wani mafarin dan adam kuma muna kira ga gwamnati da ya bayyana wannan yankin tarihi inda aka gano wadannan sauran kasusuwan Australopithecus afarensis," in ji madam Mbua.
Wannan binciken an shirya shi tare da masanan Kenya, Faransa, Japan da kuma Amurka a tudun Ngong dake kusa da birnin Nairobi. Kuma wannan karo na farko da gano Australopithecus afarensis a kasar Kenya. (Maman Ada)