in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan na fatan hada gwiwa da Sudan ta kudu wajen bunkasa hakar ma'adanai
2016-06-12 12:17:28 cri

Ministan harkokin ma'adanai a Sudan ta kudu Taban Deng, ya bayyana aniyar kasar sa game hadin gwiwa da makwafciyar ta Sudan, wajen raya fannin hakowa da cinikayyar ma'adanai, a gabar da ake fuskantar raguwar farashin danyen mai, da kuma bunkasar farashin zinari.

Mr. Deng ya yi wannan tsokaci ne a ranar Asabar, yayin da ya isa birnin Khartoum, tare da tawagar wakilai daga kasar sa, inda suka ziyarci wasu yankuna da ake hakowa da sarrafa ma'adanai. Ya ce, ziyarar da suka kai Sudan za ta karfafa kudurin kasashen biyu, game da aiwatar da dabarun bunkasa wannan sana'a.

A nasa bangare, ministan ma'adanan kasar Sudan Ahmed Mohamed Sadiq Al-Karuri, ya ce, kasar sa na cikin kasashe da ke sahun gaba wajen cinikayyar ma'adanai, tana kuma janyo jarin waje mai tarin yawa.

A watanni 3 na farkon wannan shekara, yawan zinari da Sudan ta hako ya kai tan 22.3, adadin da ya karu da kaso 3 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar bara.

Mahukuntan Sudan dai na hasashen karuwar yawan zinari da kasar ke hakowa zuwa tan 100 a wannan shekara, wanda hakan zai sanya kasar zama ta biyu a fagen samar da zinari a fadin nahiyar Afirka, kuma ta tara a tsakanin kasashen duniya.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China