Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun cimma ra'ayin sake bude iyakokin kasashensu, da kuma sake sabinta wata yarjejeniya kan jigilar man fetur tsakanin kasashen biyu, lamarin da zai taimakawa Sudan ta Kudu, yin amfani da bututuwan man fetur na kasar Sudan domin fitar da man fetur din da take samarwa, in ji jami'an Sudan ta Kudu a ranar Talata.
Bangarorin biyu sun kai ga cimma wannan yarjejeniya a albarkacin ziyarar da wata tawagar Sudan ta Kudu ta kai a kasar Sudan, a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa Taban Deng Gai.
Mista Gai ya tattauna a ranar Litinin tare da shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir kan batutuwa da dama, da suka hada da tsaro, huldar dangantaka da kuma yarjejeniyar man fetur tsakanin kasashen biyu.
Ministan tsaron kasar Sudan ta Kudu, Kuol Manyang Juk ya bayyana cewa, kasashen biyu dake makwabtaka da juna sun cimma ra'ayin sake bude iyakokinsu a cikin kwanaki 21 masu zuwa, kana kuma Sudan ta Kudu ta tabbatarwa Sudan cewa, ba za ta barin 'yan tawayen Sudan su samun gindin zama a kasarta ba.
Mista Juk ya tabbatar da cewa, Sudan ta yi kuma alkawarin samar da hatsi domin taimakawa al'ummomin Sudan ta Kudu dake cikin matsi sosai. (Maman Ada)