Ya jaddada cewa gwamnatin kasar Sin a shirye take wajen mayar da Guinee-Bissau wata babbar kasar dake fitar da shinkafa, kayayyakin cimaka na yau da kullum na al'ummar wurin wadanda har yanzu kasar sai ta shigo da su domin cike gibin abin da take nomawa.
Sin a shirye take wajen mayar da Guinee-Bissau wani runbun cimaka, in ji jakada Wang Hua, da ya nuna cewa bisa taimakon fasahohin zamani na kasar Sin, noman shinkafa a Guinee-Bissau ya karu sosai wanda ya tashi daga ton biyu zuwa ton bakwai a kowace kadada.
A cikin wannan tsarin, mista Wang ya sanar da cewa wasu kwararrun aikin gona kusan talatin na kasar Guinee-Bissau za su je kasar Sin inda za'a horar da su a fannin harkokin aikin gona da amfani da fasahohin zamani wajen samar da shinkafa.
Jakadan kasar Sin ya kuma gabatar da jerin nasarorin da aka samu bisa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, inda aka fi mai da kasar fi a fannin noma, ilimi, kiwon lafiya da kamun kifi.
Haka kuma ya bayyana cewa wani kamfanin kamun kifi na kasar Sin zai kafa masana'anta a nan gaba a kasar Guinee-Bissau, kuma zai samar da ayyukan yi na kai tsaye kusan dari hudu. (Maman Ada)